Imani Da Gaibu A Musulunci
See other videos from same category
Alhakin Zumunci A Musulunci
Kuma ka tuna lokacin da Muka xauki alqwari daga Banu Isra’ila cewa, ba za ku bauta wa kowa ba sai Allah, kuma za ku kyautata wa iyaye da makusanta da marayu da miskinai, kuma ku riqa yi wa mutane kyakkyawar magana, kuma ku tsai da salla, kuma ku ba da zakka, sannan sai kuka ba da baya sai ‘yan kaxan daga cikinku, alhalin kuna masu bijirewa
Idan kuma suka haxu da waxanda suka yi imani sai su ce: “Mun yi imani.” To amma idan suka kevanta da shaixanunsu (iyayen gidansu)[1] sai su ce: “Mu fa lalle muna nan tare da ku, mu kawai izgili ne muke yi.” Allah Yana yi musu izgili, kuma Yana yi musu talala cikin shisshiginsu suna masu ximuwa
Ta yaya?! (haka zai faru) alhali idan suka yi nasara a kanku ba za su duba wani kusanci ba balle wani alqawari game da ku? Suna yardar da ku ne da bakunansu, alhali kuwa zukatansu suna qi. Yawancinsu kuma fasiqai ne
Haxarin Munafunci A Cikin Al'umma
Idan munafukai suka zo maka sai suka ce: “Muna shaidawa cewa lalle kai Manzon Allah ne.” Allah kuma Yana sane da cewa kai tabbas Manzonsa ne, kuma Allah Yana shaidawa cewa munafukai tabbas qarya suke yi