Me Yasa Musulunci Yake Xaukar Buatar Wanin Allah
Musulunci yana ganin bauta haqqi ne tsantsa na Allah, domin shi kaxai ne wanda ya yi halitta kuma yake tafiyar da lamarinta kuma shi ne mamallakin dukkan komai.
Saboda haka roqar wanin Allah abin da babu mai iya yin sa in ba Allah ba, ko neman agajin wanin Allah cikin abin da babu wanda zai iya yin sa in ba Allah ba, ko sanya wani ya zama abokin tarayya tare da shi a ibada, ake lissafa shi a matsayin shirka.
Alqur’ani ya bayyana halin waxanda suka bautawa wanin Allah, ya ce:
“Suka kuma riqi wasu ababen bauta ba Allah ba, don a taimaka musu. Ba za su iya taimakon su ba, su da gumakan nasu duka ababen tattarawa ne (cikin wuta).”. [Yasin: 74-75]
Abin da Alqur’ani ya kawo mai sauqin fahimta ne: wanda ba ya mallaka wa kansa amfani ko cuta, ba zai yiwu ya zama wanda ya cancanci a bauta masa ba.
Saboda haka ne Musulunci ya yi watsi da bautar gumaka, ko mutane ko kuma duk wani xan tsakiya da za a nufata da abin da yake cikin abubuwan da ibada ta kevanta da su.
Daga nan ne aka samu cewa, dukkan da’awar da annabawa suka zo da ita xaya ce, watau mutane su bauta wa Allah shi kaxai, ba tare da abokin tarayya ko wani xan tsakiya ba. Domin ibada ba ta kasancewa sai ga wanda ya mallaki halitta da al’amarinta gaba xaya.
Bidiyoyi masu alaka
See other videos from same category