Allah ya ce: “Haqiqa kuma Mun halicci mutum,"

Allah ya ce: “Haqiqa kuma Mun halicci mutum,"

Allah ya ce: “Haqiqa kuma Mun halicci mutum, kuma Mun san abin da ransa yake saqa masa”. [Qaf: 16]
Wani lokaci baka buqatar abubuwan da za su warware maka matsaloli, abin da kake buqata kawai shi ne wanda zai saurareka ba tare da ya yanke sauraron naka ba.
Ka suranta cewa akwai wanda yake sauraron abin da baka kai ga furta shi ba, kuma yana ganin abin da zai biyo bayan abin da za ka kalla wanda baka kai ga furta shi ba. Yana kuma fahimtar abin da ba za ka iya yin bayaninsa ba koda ga kanka ne.
“Haqiqa kuma Mun halicci mutum, kuma Mun san abin da ransa yake saqa masa”.
Wannan ba falsafa ba ce, wannan alqawari ne.
Ba kai kaxai ba ne, kuma ba za ka tava zama a cikin duhu ba na tsawon lokaci.
Alqur’ani ba zai jiraka sai ka zama abin buga misali ba, kai dai kawai ka zama mai gaskiya yayin da kake binciken gaskiyar.
Ka karanta shi yayin da kake cikin matsi, za ka ji kamar kana sauraron wanda yake cewa da kai: Ni na sanka, kuma zan ci gaba da kasancewa tare da kai.

14
Video Translations
Saukewa
  • Hd Version ( Google Drive )

Yi tarayya