Babu Tilastawa A Addini
Ayoyi masu girma a cikin Alkur’ani ba su gushe ba wurin bayyana ma’anoni masu zurfi wadanda suke haska zuciyoyin Musulmi, suna kuma karantar dasu tushen addininsu da mu’amalolinsu. Daga cikin mafi bayyanar ayoyin da suke dauke da darussa masu tarin yawa, akwai wannan ayar, wadda Allah Ta’ala yake cewa;
Babu tilastawa a addini, haqiqa shiriya ta riga ta bayyana daban da vata. Don haka duk wanda ya kafirce wa Xagutu, kuma ya yi imani da Allah, to haqiqa ya yi riqo da igiya mafi qarfi wadda ba ta tsinkewa. Kuma Allah Mai ji ne, Masani. [Bakara: 256]
Wannan ayar wadda ake yawan tattaunawa a kanta, tana dauke da wadansu manya-manyan ma’anoni wadanda suke da alaka da ‘yancin yin addini, da hakkin mutum na zabar akidarsa ba tare da tilastawa ba. Wannan ya sanyata ta za mo cikin ayoyin masu muhimmanci game da hukunce-hukuncen Musulunci wadanda suke da alaka da hakkokin dan’adam. Da yawa daga cikin masu son zuciya sun yi kokarin yin amfani da wannan ayar wurin
da’awar cewa, ta ci karo da wasu ayoyin wadanda suke umarni da a kashe kafirai, ko kuma yin hukunci da shari’ar Allah, sai dai basu san ingantacciyar ma’anar ayar ba a siyakinta na shari’a.
Fahimtar ayar: “Babu tilastawa a addini”.
Yayin da muka yi tadabburin ayar, za mu ga abin da ake nufi da, “Babu tilastawa a addini”, shi ne, bai halatta a tilastawa wani ya shiga addinin Musulunci ba. Musulunci shi ne addinin gaskiya, kuma dalilan da suke tabbatar da gaskiyarsa a bayyane suke a sarari. Don haka duk wanda shiriya ta bayyana a gareshi daga bata, ya zabi imani da Allah, to wannan shi ne zabin mutanen kirki wadanda suke zabar alheri bisa ‘yantacciyar iradarsu.
Ba da amsa ga mabiya son zuciya game da tufka da warwarar da suke riyawa game da ayar!
Daga cikin wadanda suke riki wannan ayar a matsayin tushe ta da’awar tabbatar da tufka da warwara a cikin Alkur’ani, akwai wanda ya kafa hujja da ita don jingina karerayi game hukunce-hukuncen kisa a Musulunci, don haka suka sa hakan ya zama hanya ce ta sukar shari’ar Musulunci.
Sai dai a hakikanin lamari, babu wata tufka da warwara a cikin Alkur’ani. Don haka abin da wasu suke kawowa a matsayin tufka da warwara karancin fahimta ne a bisa hakikanin lamari.
Ba ma haka ba, ayar ba ta cin karo da kiraye-kirayen jihadi ko waninsa daga cikin hukunce-hukuncen shari’ar Musulunci ba.
Musulunci ba ya tilastawa wani yin imani, sai dai yana yin kira zuwa ga gaskiya ta hanyar hikima da wa’azi mai kyau. Don haka duk wanda ya zabi ya kawar da kansa ga barin wannan gaskiyar, to zai samu makomar zabinsa, ita ce azaba a lahira.
Don haka, Allah Mai girma da daukaka a fadinsa:
Ka ce: “Ya ku mutanena, ku yi aiki a kan irin hanyarku, lalle ni ma mai yin aiki ne (kan hanyata); don haka da sannu za ku san wanda zai yi kyakkyawan qarshe. Lalle su dai azzalumai ba za su rabauta ba. [An’am: 135]
Bidiyoyi masu alaka
See other videos from same category