Me Annabi Isa (A.S) ya Faxa Game da Kansa?

Me Annabi Isa (A.S) ya Faxa Game da Kansa?

Nana Maryam ta dawo wurin mutanen ta tana xauke da xanta a hannunta. Sai suka kalle ta suka tambaye ta, sannan suka tuhume ta. Sai dai ba ta yi wata doguwar jayayya da su ba, abin da ta yi kawai shi ne, ta yi nuni zuwa ga jaririn, sai suka ce: “Ta qaqa za mu yi magana da wanda yake xan jariri cikin shimfixar jego?” [Maryam: 29]
Sannan sai mu’ujiza ta auku, Annabi Isa ya yi magana yana jariri. Sai ya zamana farkon kalmar da ya fara furtawa wadda Alqur’ani ya naqalto ita ce; “Lalle ni bawan Allah ne, Ya ba ni littafi Ya kuma sanya ni Annabi. “Ya kuma sanya ni mai albarka a duk inda nake, kuma Ya umarce ni da yin salla da kuma ba da zakka matuqar ina raye. “Kuma mai biyayya ga mahaifiyata, bai kuma sanya ni mai girman kai mai savo ba. [Maryam: 30-32]
Wannan shi ne hoton da Alqur’ani yake gabatarwa game da Annabi Isa (A.S), Almasihu xan Maryamu, Annabi daga cikin annabawan Allah, Mai albarka a duk inda ya kasance, mai biyayya ga mahaifiyarsa, kuma mai kira zuwa ga bautar Allah. kuma za ta iya yiwuwa ka saurari qissar Annabi Isa da Nana Maryam da yawa, sai dai kuma akwai wata tambaya da ya kamata a yi ta cikin nutsuwa cewa, shin akwai ranar da ka tava karanta qissar su a bisa tsarin yadda Alqur’ani ya ba da labarin?

7
Video Translations
Saukewa
  • Hd Version ( Google Drive )

Yi tarayya