Yayin da Labarin Abin da ba Zai Tava Yiwuwa ba ya zo Mata!

Yayin da Labarin Abin da ba Zai Tava Yiwuwa ba ya zo Mata!


 

Nana Maryam ta kasance wadda ta yi nisa da iyalin ta, tana wani wuri natsattse a yayin da wani xan aike daga Allah Ta’ala ya zo mata xauke da wani labari wanda ba mai sauqi ne ga mutum ya iya sawwara shi a rayuwar sa ba, ya ce da ita: “Ni manzo ne kawai na Ubangijinki na zo don in yi miki baiwar xa tsarkakakke Maryam: 19
Sai ya zamana tambayar da ta yi tambaya ce ta xabi’a kuma ta gaskiya cewa: “Ta ce: “Ta qaqa zan samu xa, alhalin kuwa wani namiji bai tava shafa ta ba, kuma ni ban zamanto mazinaciya ba?” [Maryam: 20]. Ta yaya za ta samu xa alhali ita ba ta tava yin aure ba kuma wani namiji bai tava shafa ta ba? To sai amsa ta zo mata da cewa: “(Mala’ika) ya ce: “Kamar haka ne Ubangijinki Ya faxa (cewa): “Shi (wannan) mai sauqi ne a wurina, kuma don Mu mayar da shi aya ga mutane da kuma rahama daga gare Mu.” [Maryam: 21]
A cikin Alqur’ani, haihuwar Annabi Isa (A.S) ba abu ne da ya faru irin yadda yake faruwa a al’adance ba. Haihuwar sa aya ce da mu’ujiza daga Allah kuma rahama ce ga mutane. Qissar ba ta na kira ba ne zuwa ga tambayar, yaya aka yi haka ta faru ba ne kawai, a’a tana yin kira ne zuwa ga tambayar da ta fi wannan zurfi, wato, me ya sa Allah Ta’ala ya sanya wannan haihuwar ta zama aya ga mutane? Kuma me yake so mutum ya fahimta daga gare ta

12
Video Translations
Saukewa
  • Hd Version ( Google Drive )

Yi tarayya