Ta Ina Kowane Abu ya Fara?

Ta Ina Kowane Abu ya Fara?

Shin ka tava tambayar kanka watarana cewa, ta ya ya rayuwarka ta faro?
Ba farawa ta gaba xaya ba, a farawar karan-kanka.
Alqur’ani yana tambaya cikin nutsuwa. Shin duk wannan ya faru ne haka kawai ba tare da dalili ba?
Allah Ta’ala ya ce: “Ko kuwa an halicce su ne ba da wani mai halitta ba, ko kuwa su ne masu halittar (kansu)? Ko kuwa su suka halicci sammai da qasa? A’a, ba sa dai sakankancewa ne.” [Xur: 35-36]
Tambaya ce taqaitacciya, amma kuma ba za a iya guje mata ba.
Jikinka ba haka kawai ya samu ba, hakanan zuciyarka tana bugawa ne cikin tsari. Hankalinka yana yin tunani, yana yin tambaya, sannan kuma yana yin bincike.
Duk wani abu da ke jikin ka yana nuna ma’anar wani abu ne.
Mu ba ababen samarwa ba ne da zai zo ya wuce haka kawai ba ne. Kuma ba lambobi ba ne kawai a wannan duniyar.
Akwai mafarar mu, akwai kuma sababin samuwarmu.
Abu mafi muhimmanci shi ne mu san cewa, akwai manufar samar da mu.
Alqur’ani ba ya tilasta maka yin imani, sai dai yana kiran ka da ka yi tunani a hankali da kuma gaskiya. Saboda amsar da za ka samu za ta iya canja komai.

11
Video Translations
Saukewa
  • Hd Version ( Google Drive )

Bidiyoyi masu alaka

See other videos from same category

icon

Yi tarayya