Alkawurra da Gargadi
See other videos from same category
Muhammadu Manzon Allah ne. Waxanda kuma suke tare da shi masu tsanani ne a kan kafirai, kuma masu tausayin junansu ne; za ka gan su suna ruku’i suna sujjada suna neman falala daga Allah da yardarsa; alamominsu na gurbin sujjada suna bayyana a fuskokinsu. Wannan shi ne misalinsu a cikin Attaura. Misalinsu kuwa a cikin Linjila kamar shuka ce da ta fi...
Lalle Allah Ya sayi rayuka da dukiyoyin muminai daga wurinsu cewa suna da Aljanna: Za su yi yaqi saboda Allah, sai su kashe su ma kuma a kashe su. Alqawari ne na gaskiya da Ya xaukar wa kansa a cikin Attaura da Linjila da Alqur’ani. Wane ne ya fi Allah cika alqawarinsa? Saboda haka sai ku yi farin ciki da cinikin nan naku da kuka yi da Shi. Wannan...
Ubangijinku kuma Ya ce: “Ku roqe Ni zan amsa muku. Lalle waxanda suke yin girman kai game da bauta min, ba da daxewa ba za su shiga Jahannama a wulaqance.” Allah ne wanda Ya halitta muku dare don ku natsu a cikinsa, rana kuma don ku ga (yadda za ku yi harka). Lalle Allah Mai falala ne ga mutane, sai dai kuma yawancinsu ba sa godewa
Yin Aiki Tukuru da Kokari
Lalle Ubangijinku Shi ne Allah wanda Ya halicci sammai da qasa cikin kwana shida, sannan Ya daidaita a kan Al’arshi[1]; Yana tsara al’amari (yadda Ya ga dama). Babu wani mai ceto sai da izininsa. Wannan Shi ne Allah Ubangijinku. To sai ku bauta masa. Ashe ba za ku wa’azantu ba?
Halittun da ba a gani