Ubangijinka Ba Zai Bar ka Ba."
Ubangijinka Ba Zai Bar ka Ba
Za ta iya kasancewa watarana ka yi sujjada har ka zubar da hawaye, ka gama sallarka amma ba ka gushe ba kana jin kana cikin kaxaici.
Amma fa hakan a yadda kake ji ne kawai, ba wai shi ne a haqiqanin lamari ba.
Allah Ta’ala ya ce da masoyinsa (S.A.W): “Ubangijinka bai bar ka ba kuma bai qi ka ba”.
To ina ga wanda ya bi shi, ya kuma yi riqo da Alqur’aninsa?
Ba a manta da kai ba, kuma ba ka yi nisa daga ganin Allah ba.
Idan ka ji a ranka cewa babu mai ganinka, to ka sani cewa Allah bai rafkana game da kai ba gwargwadon qiftawar ido.
Ka karanta Suratud Duha da tadabburi.
Ba kamar yadda mai karatu cikin sauri yake karatu ba, a’a karatu irin na wanda yake jiran amsa daga sama.
Alqur’ani ba da magana kawai yake ba da nutsuwa ba, a’a yana lallashin zuciyarka yana cewa da kai, ina tare da kai, ba zan bar ka ba har abada.
Bidiyoyi masu alaka
See other videos from same category