See other videos from same category
Kuma (ka tuna) ranar da za Mu tayar wa kowace al’umma da mai ba da shaida a kansu daga jinsinsu, Mu kuma zo da kai (Annabi Muhammadu) shaida a kan waxannan (wato al’ummarka). Kuma Mun saukar maka da Littafi ne (wato Alqur’ani) don bayani ga kowanne abu, kuma shiriya da rahama da bushara ga Musulmi
Sai Musa ya jefa sandarsa, sai ga ta tana lanqwame duk abin da suke qagowa (na sihiri) Sai aka durqusar da masu sihirin suna masu sujjada Suka ce: “Mun yi imani da Ubangijin talikai
Lalle waxanda suka yi imani suka kuma yi aiki na gari, to (Allah) Mai rahama zai sanya musu qauna
k
Kuma kamar haka ne Muka yiwo maka wahayin Ruhi (watau Alqur’ani) daga umarninmu. Ba ka zamanto ka san mene ne littafi ko kuma imani ba, sai dai kuma Mun sanya shi (Alqur’ani) haske ne da Muke shiryar da wanda Muka ga dama daga bayinmu da shi. Lalle kuma kai tabbas kana shiryarwa zuwa ga tafarki madaidaici
Kissoshin Shiriya a Cikin Alƙur ani