Kakaci ne Kawai – Musulmi

Kakaci ne Kawai – Musulmi

A zamantakewar abokai, xaya daga cikin su yana koyon yaren abokin sa da ya zo daga wani Garin.
Kowa yana yin dariya, amma shi abokin yana yin murmushi. Sai dai ba mu san me ke voye a bayan murmushin ba.
Za mu iya cewa, ai wannan kakaci ne kawai. Amma shin mun tambaye shi mun ji yaya ya ji wannan abin?
Mu karanta wannan ayar a cikin littafin Allah:
“Ya ku waxanda suka yi imani, kada wasu mutane su yi wa wasu mutane izgili, mai yiwuwa ne su zamanto sun fi su alheri, kuma kada wasu mata (su yi wa) wasu mata (izgili), mai yiwuwa ne su zamanto sun fi su alheri; kada kuma ku riqa aibata junanku, kuma kada ku riqa jifan juna da munanan laquba (da kuke qi). Tir da sunan fasiqanci bayan imani. Wanda duk bai tuba ba, to waxannan su ne azzalumai.” [Hujurat: 11]
Kafin mu shiga cikin masu yin dariyar, mu xan tsaya kaxan. Za mu iya canja tsarin yadda ake tattaunawar, shi ne cewa, mu tambaye shi mu ji ra’ayin sa, mu kuma ba shi dama ya yi magana ba tare da mun kwaikwaye shi ba.
Idan kuma har mun cutar da shi, to mu nemi yafiyar sa, ba tare da mun ce kai mutum ne mai saurin hasala ba.
Ya Ubangiji, ka sanar da mu yadda za mu riqa yin farin ciki tare da mutane, ba tare da mun vata musu rai ba.

40
Video Translations
Download
  • Hd Version ( Google Drive )

Subscribe To Get New Updates