Yaruka Masu Yawa."
Waxanda ba Musulmi ba
Yayin da ake zaune a wurin jira a filin jirgi, za ka ji yarukan da ba ka fahimtar su.
Amma kuma kana fahimtar hawayen bankwana, hakanan kana yin murmushi ga yaron da yake sauri yana nufatar wanda yake jiransa.
Ba ka san sunan su ba. Amma tare da haka, wani abu da yake sananne a gare ka yana bayyana a tare da su.
An ambaci yarukan mutane da launukan su tare da halittar sammai da qasa a cikin Alqur’ani tare da siffanta su da cewa ayoyi ne da suke kira zuwa ga yin tuntuni game da qudurar Allah.
Allah Ta’ala ya ce: “Yana kuma daga cikin ayoyinsa halittar sammai da qasa da kuma sassavawar harsunanku da launukanku. Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi ga ma’abota ilimi.” [Rum: 22]
Ka riya yadda za ka kalli savanin ka da wasu da wannan idon.
Ba sai ka voye yaren ka ba, kuma ba sai ka nemi su zama makwafin ka ba.
Za ka iya tambayar ma’anar sunan abu, ko kuma ka koyi sanin wata sabuwar kalma, sannan ka saurara ka ji me take xauke da shi na labari.
Zai iya kasancewa mutumin da yake nesa da kai ya fi kusanci da kai sama da yadda kake tsammani.
Yin tuntuntuni game da sassavar fuskoki zai iya kai ka ga yin wata sabuwar tambaya cewa, wane ne ya halicce su?
Related Videos
See other videos from same category