Imani Da Gaibu A Musulunci
See other videos from same category
Ta yaya?! (haka zai faru) alhali idan suka yi nasara a kanku ba za su duba wani kusanci ba balle wani alqawari game da ku? Suna yardar da ku ne da bakunansu, alhali kuwa zukatansu suna qi. Yawancinsu kuma fasiqai ne
Kuma ka tuna lokacin da Muka xauki alqwari daga Banu Isra’ila cewa, ba za ku bauta wa kowa ba sai Allah, kuma za ku kyautata wa iyaye da makusanta da marayu da miskinai, kuma ku riqa yi wa mutane kyakkyawar magana, kuma ku tsai da salla, kuma ku ba da zakka, sannan sai kuka ba da baya sai ‘yan kaxan daga cikinku, alhalin kuna masu bijirewa
Ka ce: “Lalle Ubangijina Yana shimfixa arziki ga wanda Ya ga dama, Ya kuma quntata, sai dai kuma yawancin mutane ba su san (haka) ba.”
Waxanda kuma ba su sami wadatar yin aure ba su kame kansu har Allah Ya wadata su daga falalarsa. Waxanda kuwa suke neman fansar kansu daga bayinku[1], sai ku ba su damar fansar kansu, idan kun san suna da halin iya biya; kuma ku ba su wani abu daga dukiyar Allah da Ya ba ku. Kada kuma ku tilasta wa kuyanginku ‘yan mata a kan yin zina idan sun nemi...
Idan kuma suka haxu da waxanda suka yi imani sai su ce: “Mun yi imani.” To amma idan suka kevanta da shaixanunsu (iyayen gidansu)[1] sai su ce: “Mu fa lalle muna nan tare da ku, mu kawai izgili ne muke yi.” Allah Yana yi musu izgili, kuma Yana yi musu talala cikin shisshiginsu suna masu ximuwa
Haxarin Munafunci A Cikin Al'umma