Tsare Amana Tsare Rayuwa Ne
See other videos from same category
Idan kuma wasu qungiyoyi biyu na muminai suka yaqi junansu sai ku yi sulhu a tsakaninsu; to idan xayarsu ta yi ta’adda a kan xayar, to sai ku yaqi wadda ta yi ta’addar har sai ta komo zuwa bin umarnin Allah. Idan ta komo sai ku yi sulhu a tsakaninsu bisa adalci, ku kuma yi adalci; lalle Allah Yana son masu adalci
Kuma sakamakon mummunan (abu) shi ne mayar da mummuna kamarsa; to wanda ya yi afuwa ya kuma kyautata, to ladansa yana wurin Allah. Lalle Shi ba Ya son azzalumai
Farin Cikin Haquri
Ku Za Mo Cikin Masu Gaskiya A Kowane Yanayi
Ya ku waxanda suka yi imani, duk wanda ya yi ridda daga cikinku, ya bar addininsa, to (ya sani) Allah zai kawo waxansu mutane da Yake son su suna son Sa, suna masu qasqantar da kai ga muminai, suna masu nuna wa kafirai isa, suna yin jihadi don xaukaka kalmar Allah, kuma ba sa jin tsoron zargin wani mai zargi. Wannan falalar Allah ce da Yake bayar d...
Bayin (Allah) Mai rahama kuwa (su ne) waxanda suke tafiya a bayan qasa a natse; idan kuma wawaye sun yi musu magana (sai) su faxa (musu) magana ta aminci