A Kan Dokin Qofar Gidanka"

A Kan Dokin Qofar Gidanka"

Ka xauka cewa ka tashi ka koma sabon gida.
A cikin wani yini mai sanyi....sai ga maqocin ka yana qwanqwasa qofa, yana xauke da abinci. Kai da shi ba ku wani san juna ba sosai, kuma daga mabambantan garuruwa ku ke. Wataqila ma ba addinin ku xaya ba.
Sai dai wannan yanayin zai sa wurin ya zama mai qarancin jin baqunta.
A cikin Alqur’ani akwai maganar kyautatawa da yin adalci ga wanda ba su yaqi Musulmi a addini ba kuma ba su fitar da su da gidajen su ba.
Allah Ta’ala ya ce: “Allah bai hana ku ba game da waxanda ba su yaqe ku don addini ba ba su kuma fitar da ku daga gidajenku ba, kan ku kyautata musu, ku kuma yi musu adalci. Lalle Allah Yana son masu adalci.” [Mumtahana: 8]
Al’birru shi ne ku kyautata musu, Al’qisxu shi ne ku yi musu adalci.
Sanayya za ta iya kasancewa ta hanyar ba da abinci, sannan tambayar ya iyalai suke da kuma tambaya ta gaskiya game da abin da mutum yake qudurcewa na aqida.
Ba dole ne sai an tambayi duk abin da ake so a tambaya ba a haxuwa xaya, ka ba wa tattaunar lokaci.
Zai iya kasancewa sanin ka da Alqur’ani zai fara ne ta wannan tambayar.
Me zai faru idan muka rayu tare da irin wannan ma’anar?

45
Video Translations
Download
  • Hd Version ( Google Drive )

Related Videos

See other videos from same category

icon

Subscribe To Get New Updates