Saboda me Musulunci Yake Tsawatarwa Game da Jivinta."

Saboda me Musulunci Yake Tsawatarwa Game da Jivinta."

Wataqila wanda ba Musulmi ba zai yi tambaya ya ce, me ya sa Alqur’ani yake tsawatarwa game da jivintar kafirai?
Amsar ita ce, manufar ba ita ce a hana mu’amala ko yin adalci ko kyautatawa waxanda ba Musulmi ba. Waxannan abubuwa ne da Musulunci ya tabbatar da su. Sai dai abin da ake nufi shi ne a hana jivinta ta qudiri da aqida wanda zai sa mutum ya bi varna ko ya riqa qarfafarta ko ya riqa gabatar da varna a kan gaskiya. Saboda haka ne ma Alqur’ani yake cewa:
“Kada muminai su riqi kafirai a matsayin masoya su qyale muminai;”. [Ali Imran: 28]
Sannan ya bayyana sakamakon bin mavarnata, ya ce:
“Kaicona ina ma da ban riqi wane aboki ba!”. [Furqan: 28]
Saqon a nan, saqo ne na duniya baki xaya: mutum ya sani cewa za a tambaye shi game da zavinsa. Don haka bai kamata ya sanya jivintar sa ga wasu mutane ba ko wasu tunane-tunane ba waxanda za su nesanta shi daga gaskiya ba.
Shi ya sa Musulunci yake kiran kowane mutum da ya riqa binciken haqiqanin gaskiya da kansa, ya nisanci abin da al’umma za ta matsa masa a kansa ko kuma bin wasu ido rufe.

النص

39
Video Translations
Saukewa
  • Hd Version ( Google Drive )

Yi tarayya