Ɗaya Tamkar Ƙasa: Lokacin da Mutum Ɗaya ke Haifar da Tasirin Dukan Ƙungiyar Musulmi (Ummah)
Masu gaskiya na hakika suna bayyana ne a lokutan tsanani. Mutum ne ba a san sunansa ba, amma matsayar da ya dauka ta sa ya tseratar da Annabi.
Mutum daya tamkar al'ummas
Idan ba don wasu daga cikin al'umma na baya sun hana barna a ƙasa ba, da an rusa komai gaba ɗaya, amma Allah Ya ceci kaɗan daga cikinsu. Ya Allah, Ka sanya mu daga cikin masu gyara!
Sai wani mutum (mumini daga mutanen Fir’auna) ya zo daga can qarshen birnin yana gaggawa, ya ce: “Ya Musa, lalle manyan gari (suna can) suna shawara a kanka don su kashe ka, to ka fita (daga birnin nan), lalle ni ina cikin masu yi maka nasiha.” [Qasas: 20]
Masu gaskiya na hakika suna bayyana ne a lokutan tsanani. Mutum ne ba a san sunansa ba, amma matsayar da ya dauka ta sa ya tseratar da Annabi.
Nasiha ta gaskiya a lokacin da ta dace za ta iya canja makomar al’umma.
Sai wani mutum (mumini daga mutanen Fir’auna) ya zo daga can qarshen birnin yana gaggawa, ya ce: “Ya Musa, lalle manyan gari (suna can) suna shawara a kanka don su kashe ka, to ka fita (daga birnin nan), lalle ni ina cikin masu yi maka nasiha.” [Qasas: 20]
Kada ka jira sai ka zama wani shahararre kafin ka samar da wani tasiri a cikin al’umma.
Ya isa ka kasance mai gaskiya, mai juriya, mai tsantsanta nasiharka, tarihi zai iya dawwamar da matsayarka ba sunanka ba.
Wani mutum kuma ya zo daga can qarshen gari yana sauri ya ce: “Ya ku mutanena, ku bi waxannan manzannin.”. [Yasin: 20]
Yayin da mutum yake jin cewa akwai nauyin shiriya a kansa, ba zai jira wani kira ko izini ba, a’a kawai zai zabura ne da kansa don ya farkar da gafalallu.
Yin rigegeniya wurin aikata alheri shi ke samar da canji, ko da kuwa ka kasance kai kadai ne.
Wani mutum kuma ya zo daga can qarshen gari yana sauri ya ce: “Ya ku mutanena, ku bi waxannan manzannin.”. [Yasin: 20]
Kai waye ko daga ina kake, ba shi ne abu mai muhimmanci ba. Abu mai muhimmanci shi ne, me kake dauke dashi na da’awa, kuma ya makurar gaskiyarka take na isar da ita?
Mazaje na gaske suna kokari wurin yada haske a lokacin duhu.
Ka ce: “Lalle sallata da yankana da rayuwata da mutuwata, duk na Allah ne Ubangijin talikai. [An’am: 162]
Yayin da manufarka a rayuwa ta zama ita ce Allah, to dukkan ayyukanka na al’ada za su juya su koma ibada...don haka sai a wayi gari sallarka da kai-kawonka har lokacin da za ka mutu su zamana hanya ce zuwa gare shi.
Ka ce: “Lalle sallata da yankana da rayuwata da mutuwata, duk na Allah ne Ubangijin talikai. [An’am: 162]
Ikhlasi na hakika ba abu ne na dan lokaci ba, a’a shi hanyar rayuwa ce, yana farawa daga niyyarka ta salla, ya kuma ci gaba a dukkan bangarorin rayuwarka har zuwa lokacin mutuwa.
Lalle wannan Alqur’anin yana shiryarwa ne ga (hanya) mafi miqewa, yana kuma yi wa muminai waxanda suke yin kyawawan ayyuka albishir cewa, lalle suna da lada mai girma. [Isra’i: 9]
A duniyar da hanyoyi suka yawaita, kuma na’urar gano inda aka dosa ta lalace, to akwai wata hanya kwaya daya wadda take shiryarwa zuwa ga hanya mafi mikewa, babu karkata ko kaucewa a kanta...
Ka nemi haske daga littafin Allah, za ka samu hanya.
Lalle wannan Alqur’anin yana shiryarwa ne ga (hanya) mafi miqewa, yana kuma yi wa muminai waxanda suke yin kyawawan ayyuka albishir cewa, lalle suna da lada mai girma. [Isra’i: 9]
Ba alkawari ba ne irin na al’ada...a’a wannan bushara ce daga Ubangijin talikai ga dukkan Muminin da ya yi ayyuka na gari:
Lada mai yawa yana jiranka.
Wane alkawari ne ya kai wannan girma, Wane ne ya kai Ubangiji karamci.
Shin yanzu wanda ya kasance matacce (kafiri), sai Muka rayar da shi, kuma Muka sanya masa haske (na shiriya), yana tafiya da shi cikin mutane, (yanzu) zai zama kamar wanda yake cikin duhu (na kafirci), ta yadda ba zai iya fita daga cikinsa ba? Kamar haka ne aka qawata wa kafirai abin da suka kasance suna aikatawa. [An’am: 122]
Shiriya ba wai ita ce mutum ya yi sani ba kawai, a’a ita wata rayuwa ce sabuwa da take tashi a zuciya, kuma haske ne da yake haskaka maka hanya a tsakiyar duffan mutane.
Shin yanzu wanda ya kasance matacce (kafiri), sai Muka rayar da shi, kuma Muka sanya masa haske (na shiriya), yana tafiya da shi cikin mutane, (yanzu) zai zama kamar wanda yake cikin duhu (na kafirci), ta yadda ba zai iya fita daga cikinsa ba? Kamar haka ne aka qawata wa kafirai abin da suka kasance suna aikatawa. [An’am: 122]
Bambancin dake tsakanin wanda yake rayuwa bisa hasken imani da wanda ya nutse a cikin duhun gafala...kamar bambancin rayayye ne da yake tafiya bisa basira da mataccen da ba ya gani.
“(Su ne) waxanda suka yi imani , zukatansu kuma suna nutsuwa da ambaton Allah. Ku saurara, da ambaton Allah ne zukata suke nutsuwa.” [Ra’ad: 28
Qunci da damuwa ba sa gushewa ta dalilin yawan tunani, a’a suna dai gushewa ne ta dalilin tsarkake zukata...ambaton Allah shi ne mabudin samun nutsuwa ga wanda duniya ta yi wa kunci.
Sai na ce: “Ku nemi gafarar Ubangijinku, lalle Shi Ya kasance Mai yawan gafara ne. “Zai saukar muku da ruwan sama mai yawa. “Kuma Ya daxe ku da dukiyoyi da ‘ya’yaye, Ya kuma sanya muku gonaki Ya kuma gudanar muku da qoramu. [Nuh: 10-12]
Istigfari ba shi ne gafarta zunubai kawai ba, a’a shi kofar arziki ce, kuma hutun rai ne da yalwa wurin bayarwa.
Duk wanda duniya ta yi wa kunci, to ya kwankwasa kofar sama da kalma daya: wato Astagfirullah.
Sai na ce: “Ku nemi gafarar Ubangijinku, lalle Shi Ya kasance Mai yawan gafara ne. “Zai saukar muku da ruwan sama mai yawa. “Kuma Ya daxe ku da dukiyoyi da ‘ya’yaye, Ya kuma sanya muku gonaki Ya kuma gudanar muku da qoramu. [Nuh: 10-12]
Lokacin da komai ya tsaya, arziki ya yi jinkiri, alheri ya karanta...To ga addu’a nan gaba gareka: wato istigfari.
Lallai shi alkawarin Allah ne wanda ba a saba shi, kawai ka fara kuma ka tabbata.
Fir’auna kuma ya ce: “Ku bar ni in kashe Musa, kuma (ya je) ya kirawo Ubangijin nasa; lalle ni ina jin tsoron kada ya sauya addininku ko kuma ya bayyanar da varna a bayan qasa.” [Ghafir: 26]
A ko da yaushe azzalumai suna tsoron kawo canji, suna cakuda gaskiya da karya.
Fir’auna bai ji tsoron barna ba, a’a shi dai kawai ya ji tsoron gushewar mulkinsa ne idan har kalmar gaskiya ta bayyana.
Fir’auna kuma ya ce: “Ku bar ni in kashe Musa, kuma (ya je) ya kirawo Ubangijin nasa; lalle ni ina jin tsoron kada ya sauya addininku ko kuma ya bayyanar da varna a bayan qasa.” [Ghafir: 26]
A yayin da gyara ya zama barna a idon azzalumai, to ka sani amon gaskiya ne ya ratsa su, kuma ka sani da’awarka ta fara amfani.
Kuma kada ku yi varna a bayan qasa bayan gyara ta, kuma ku bauta masa kuna masu tsoro da kwaxayi. Lalle rahamar Allah a kusa take da masu kyautatawa. [A’araf: 56]
Yin barna bayan gyara kasa laifi ne a kan laifi, saboda mai yin haka yana rusa abin da aka gina na alheri.
Kada ka zama gudumar rusawa bayan ka san hanyar da aka bi aka gina.
Kuma kada ku yi varna a bayan qasa bayan gyara ta, kuma ku bauta masa kuna masu tsoro da kwaxayi. Lalle rahamar Allah a kusa take da masu kyautatawa. [A’araf: 56]
Ka roki Ubangijinka da zuciya mai cike da tsoro da fata, don kofar rahama a kusa take, sai dai ba a budeta sai ga masu kyautatawa, wadandaz suka kyautata a duniya ba su yi barna a cikinta ba.
Waxanda mala’iku suke xaukar ransu suna tsarkaka, suna cewa: “Aminci ya tabbata a gare ku, ku shiga Aljanna saboda abin da kuka zamanto kuna aikatawa (a duniya). [Nahl: 32]
Me ya kai kyakkyawar cikawa dadi, mala’iku su karbe ka da aminci, a bude maka kofar Aljanna saboda abin da ka gabatar na ayyuka na gari.
Cikawar karshe tana takaita tafiya, don haka ka zaba wa kanka abin da kake so a cika maka dashi.
Waxanda mala’iku suke xaukar ransu suna tsarkaka, suna cewa: “Aminci ya tabbata a gare ku, ku shiga Aljanna saboda abin da kuka zamanto kuna aikatawa (a duniya). [Nahl: 32]
Ayyukanka na yau su ne kalmomin da za su yi maka maraba a gobe, don haka ka shuka alheri a kowane lokaci, don zai iya kasancewa lokacin bankwana yana dab da kai sama da yadda kake zato.