Sakonnii daga Allah
zuwa ga zuciyarka:
Tafiyar shiriya
A duniyar da take cakuxe da duhu, Alqur’ani yana zuwa a matsayin wani haske da zai daidaita maka lamarinka, ba ma haka ba, sai ya nuna maka hanyar da za ka bi ka samu aminci.
Sakonnii daga Allah
zuwa ga zuciyarka:
Tafiyar shiriya
Ba daga cikin duhu xaya Alqur’ani yake fitar da kai ba, yana fitar da kai daga cikin duffai masu yawa, zuwa ga haske guda xaya kuma bayyananne.
Ya ku mutane, haqiqa gargaxi ya zo muku daga Ubangijinku da kuma waraka ga abin da yake cikin zukatanku, kuma shiriya ne da rahama ga muminai. [Yunus: 57]
Yayin da qirjinka zai yi maka nauyi kuma ba ka san dalilin da ya da kake jin raxaxin hakan ba, sai Alqur’ani ya zo maka ba don ya zarge ka ba sai dai don ya warkar da abin da ba a iya gani na cuta.
Ya ku mutane, haqiqa gargaxi ya zo muku daga Ubangijinku da kuma waraka ga abin da yake cikin zukatanku, kuma shiriya ne da rahama ga muminai. [Yunus: 57]
Alqur’ani ba rubutu ne da ake karantawa ba kawai, sai dai shi wa’azi ne da yake faxakarwa, da kuma waraka da take gyara abu, da rahama da take riqe zuciyarka cikin tausasawa.
Ya ku waxanda aka bai wa Littafi, haqiqa Manzonmu ya zo muku, yana bayyana muku da yawa daga cikin abin da kuke voyewa daga Littafin, yana kuma yin afuwa ga abubuwa da dama daga ciki. Haqiqa haske ya zo muku daga Allah, da kuma Littafi mai bayyanawa. Da shi ne Allah Yake shiryar da wanda ya bi yardarsa hanyoyi na aminci, kuma Yake fitar da su daga duffai zuwa ga haske da izininsa, kuma Yana shiryar da su zuwa ga tafarki madaidaici. [Ma’ida: 15-16]
A duniyar da take cakuxe da duhu, Alqur’ani yana zuwa a matsayin wani haske da zai daidaita maka lamarinka, ba ma haka ba, sai ya nuna maka hanyar da za ka bi ka samu aminci.
Ya ku waxanda aka bai wa Littafi, haqiqa Manzonmu ya zo muku, yana bayyana muku da yawa daga cikin abin da kuke voyewa daga Littafin, yana kuma yin afuwa ga abubuwa da dama daga ciki. Haqiqa haske ya zo muku daga Allah, da kuma Littafi mai bayyanawa. Da shi ne Allah Yake shiryar da wanda ya bi yardarsa hanyoyi na aminci, kuma Yake fitar da su daga duffai zuwa ga haske da izininsa, kuma Yana shiryar da su zuwa ga tafarki madaidaici. [Ma’ida: 15-16]
Ba daga cikin duhu xaya Alqur’ani yake fitar da kai ba, yana fitar da kai daga cikin duffai masu yawa, zuwa ga haske guda xaya kuma bayyananne.
Kuma akwai wasu mutane waxanda suke bauta wa wasu kishiyoyi ba Allah ba; suna son su kamar son Allah; waxanda kuwa suka yi imani sun fi son Allah (fiye da komai). Da a ce waxanda suka yi zalunci za su ga lokacin da suke ido huxu da azaba (to da sun gane) cewa, lalle duk wani qarfi na Allah ne gaba xaya, kuma lalle Allah Mai tsananin azaba ne. [Baqara: 165]
Yayin da zuciya ta cika da son Allah, dukkan wasu abubuwa da ake so za su zama ba wani abu ba, kuma ma’auni zai daidaita.
Kuma akwai wasu mutane waxanda suke bauta wa wasu kishiyoyi ba Allah ba; suna son su kamar son Allah; waxanda kuwa suka yi imani sun fi son Allah (fiye da komai). Da a ce waxanda suka yi zalunci za su ga lokacin da suke ido huxu da azaba (to da sun gane) cewa, lalle duk wani qarfi na Allah ne gaba xaya, kuma lalle Allah Mai tsananin azaba ne. [Baqara: 165]
Son Allah ba da’awa ba ce, sai dai zavi ne da yake canja abubuwan da aka fifita ya ‘yantar da zuciya daga rataya kanta da abin da yake ba na gaskiya ba.
Ya ku waxanda suka yi imani, duk wanda ya yi ridda daga cikinku, ya bar addininsa, to (ya sani) Allah zai kawo waxansu mutane da Yake son su suna son Sa, suna masu qasqantar da kai ga muminai, suna masu nuna wa kafirai isa, suna yin jihadi don xaukaka kalmar Allah, kuma ba sa jin tsoron zargin wani mai zargi. Wannan falalar Allah ce da Yake bayar da ita ga wanda Ya ga dama. Kuma Allah Mayalwaci ne, Masani. [Ma’ida: 54]
Mafi girman matsayin da mutum zai samu shi ne Allah ya so shi tun kafin shi ya so Allah.
Ya ku waxanda suka yi imani, duk wanda ya yi ridda daga cikinku, ya bar addininsa, to (ya sani) Allah zai kawo waxansu mutane da Yake son su suna son Sa, suna masu qasqantar da kai ga muminai, suna masu nuna wa kafirai isa, suna yin jihadi don xaukaka kalmar Allah, kuma ba sa jin tsoron zargin wani mai zargi. Wannan falalar Allah ce da Yake bayar da ita ga wanda Ya ga dama. Kuma Allah Mayalwaci ne, Masani. [Ma’ida: 54]
Yayin da Allah zai so ka, to za ka samu tabbatuwa, ba za ka ji tsoron zargi ba, ba kuma za ka siyar da gaskiya da ka sani ba.
Kuma kamar haka ne Muka yiwo maka wahayin Ruhi (watau Alqur'ani) daga umarninmu. Ba ka zamanto ka san mene ne littafi ko kuma imani ba, sai dai kuma Mun sanya shi (Alqur’ani) haske ne da Muke shiryar da wanda Muka ga dama daga bayinmu da shi. Lalle kuma kai tabbas kana shiryarwa zuwa ga tafarki madaidaici. [Shura: 52]
Alqur’ani ba shiryayyiyar amsa ba ce ba kawai, sai dai haske ne da yake abokantakarka, lokacin da kake can kana laluben wani abu.
Kuma kamar haka ne Muka yiwo maka wahayin Ruhi (watau Alqur'ani) daga umarninmu. Ba ka zamanto ka san mene ne littafi ko kuma imani ba, sai dai kuma Mun sanya shi (Alqur’ani) haske ne da Muke shiryar da wanda Muka ga dama daga bayinmu da shi. Lalle kuma kai tabbas kana shiryarwa zuwa ga tafarki madaidaici. [Shura: 52]
Yayin da tambayoyi suka yi cincirindo, to ba ka buqatar hayaniya a lokacin, sai dai kana buqatar hasken da zai yi maka jagora cikin nutsuwa.
ALIF LAM RA. Littafi ne da Muka saukar maka da shi, don ka fitar da mutane daga duffai zuwa ga haske, da izinin Ubangijinsu zuwa ga tafarkin (Allah) Mabuwayi, Abin godiya. [Ibrahim: 1]
Saqon Alqur’ani ba canja matashiyoyi ba ne, sai dai saqon Alqur’ani tseratar da mutum ne daga ximuwa.
ALIF LAM RA. Littafi ne da Muka saukar maka da shi, don ka fitar da mutane daga duffai zuwa ga haske, da izinin Ubangijinsu zuwa ga tafarkin (Allah) Mabuwayi, Abin godiya. [Ibrahim: 1]
Alqur’ani ba ya yi wa duhu ado, sai dai ma ya fitar da kai daga duhu, mataki bayan mataki.
Kuma (ka tuna) ranar da za Mu tayar wa kowace al’umma da mai ba da shaida a kansu daga jinsinsu, Mu kuma zo da kai (Annabi Muhammadu) shaida a kan waxannan (wato al’ummarka). Kuma Mun saukar maka da Littafi ne (wato Alqur’ani) don bayani ga kowanne abu, kuma shiriya da rahama da bushara ga Musulmi. [Nahl: 89]
Babu wata buqata da zuciya take da ita face Alqur’ani ya yi bayani game da ita ko kuma ya ba da wata shiriya ko ya kawo rahama game da ita.
Kuma (ka tuna) ranar da za Mu tayar wa kowace al’umma da mai ba da shaida a kansu daga jinsinsu, Mu kuma zo da kai (Annabi Muhammadu) shaida a kan waxannan (wato al’ummarka). Kuma Mun saukar maka da Littafi ne (wato Alqur’ani) don bayani ga kowanne abu, kuma shiriya da rahama da bushara ga Musulmi. [Nahl: 89]
Alqur’ani ba ya barinka a tsakiyar hanya, sai dai yana kasancewa tare da kai har sai ka samu nutsuwa.
Sai Musa ya jefa sandarsa, sai ga ta tana lanqwame duk abin da suke qagowa (na sihiri). Sai aka durqusar da masu sihirin suna masu sujjada. Suka ce: “Mun yi Imani da Ubangijin talikai. [Shu’ara: 45-47]
Lokaci guda na gaskiya ya canja tarihin masu sihiri, sai suka wayi gari sun zama cikin masu yin sujjada.
Sai Musa ya jefa sandarsa, sai ga ta tana lanqwame duk abin da suke qagowa (na sihiri). Sai aka durqusar da masu sihirin suna masu sujjada. Suka ce: “Mun yi Imani da Ubangijin talikai. [Shu’ara: 45-47]
Shiriya za ta iya zuwa ba zato ba tsammani, sannan kuma za ta iya canja dukkan wani abu da zai zo a bayanta.