Karin Magana a cikin Alqur'ani

Karin Magana a cikin Alqur'ani

Da za Mu saukar da wannan Alqur’ani ga wani dutse, da lalle ka gan shi yana mai qasqantar da kai mai tsattsagewa don tsoron Allah. Waxannan misalan Muna buga wa mutane su ne don su yi tunani[Suratul Hashr:21]

Kuma misalin waxanda suke ciyar da dukiyoyinsu don neman yardar Allah da tabbatar da (imani) a zukatansu, kamar misalin gona ce a kan jigawa sai ruwan sama mamako ya same ta, sai ta ba da amfaninta rivi-biyu. To idan mamakon ruwan bai same ta ba, sai yayyafi (ya wadatar da ita). Kuma Allah Mai ganin abin da kuke aikatawa ne[Suratul Baqara:265]

Misalin wadanda suka kafirta kamar misalin wanda yake daga sauti ne ga wanda ba ya jin (komai) sai kira da sowa. Kurame ne, bebaye ne, makafi ne, don haka su ba sa hankalta[Suratul Baqara:171]

Tana bayar da ‘ya’yanta ko da yaushe da izinin Ubangijinta. Allah kuwa Yana ba da misalai ne ga mutane don su wa’azantu[Suratu Ibrahim:25]

25 0

Yi tarayya