Rayuwarka ba don wargi aka samar da ita ba, ko wane minti xaya na rayuwa yana da manufa mai zurfi.
Muna kan hanyar tafiya ne zuwa Allah Mahalicci, kuma komawa zuwa gare shi ita ce babbar manufarmu.
Ma'anar Rayuwa a Hasken Alkur'ani
Allah ya haliccemu ne don mu bauta masa kawai, shi Mawadaci daga buqatar wani abu daga wurinmu.
Babbar munafa a rayuwarmu ba a cikin arziqi ko abinci take ba, a’a tana samun kusanci da Allah Mahalicci da bauta tagaskiya.
“(Allah Ya ce da su): “Ko
kuna tsammani ne cewa Mun
halicce ku ne ba manufa kuma
ku ba za a dawo da ku gare
Mu ba?” To Allah Sarki na
gaskiya Ya xaukaka; babu
wani abin bauta da gaskiya sai
Shi, (Shi ne) Ubangijin
Al’arshi mai girma. [Muminun: 115-116)
Rayuwarka ba don wargi aka samar da ita
ba, ko wane minti xaya na rayuwa yana
da manufa mai zurfi.
Muna kan hanyar tafiya ne zuwa Allah
Mahalicci, kuma komawa zuwa gare shi
ita ce babbar manufarmu.
“(Allah Ya ce da su): “Ko
kuna tsammani ne cewa Mun
halicce ku ne ba manufa kuma
ku ba za a dawo da ku gare
Mu ba?” To Allah Sarki na
gaskiya Ya xaukaka; babu
wani abin bauta da gaskiya sai
Shi, (Shi ne) Ubangijin
Al’arshi mai girma. [Muminun: 115-116)
Kowane mataki na rayuwarka yana da
ma’ana, kuma komawa zuwa ga Allah shi
ne maqura. Ba a haliccemu don wasa ba.
Yanz mutum yana tsammanin
za a bar shi haka sasakai?
Shin bai kasance wani xigo na
maniyyi da ake zuba shi (a
mahaifa) ba? Sannan ya zama
gudan jini sannan (Allah) Ya
halicce (shi) sai Ya daidaita
(shi)? [Alqiyama: 36-38]
Ba a halicci mutum ba ba tare da manufa
ba, tafiyarmu tana farawa ne daga
qaramin xigon maniyyi, sannan mu wayi
gari mun zama cikakkiyar halitta.
Duk da wannan ta ya ya rayuwarmu za ta
zamo babu manufa a cikin halittarta.
Yanz mutum yana tsammanin
za a bar shi haka sasakai?
Shin bai kasance wani xigo na
maniyyi da ake zuba shi (a
mahaifa) ba? Sannan ya zama
gudan jini sannan (Allah) Ya
halicce (shi) sai Ya daidaita
(shi)? [Alqiyama: 36-38]
Daga wani qaramin mataki da ba a iya
gani, zuwa matakin mutum da yake iya ji
yake gani yake kuma yin tunani.
Kuma ga Allah ne mulkin
sammai da qasa yake. Kuma
Allah Mai iko ne a kan komai.
Lalle a cikin halittar sammai
da qasa da sassavawar dare da
rana, tabbas akwai ayoyi ga
ma’abota hankula. [Ali Imran:
189-190]
Ka kalli sama da qasa da jujjuyawar dare
da yini, wannan tsarin da suke tafiya a kai
ba haka kawai ya faru ba, a’a tsari ne na
Allah Mahalicci wanda ya mallaki duniya
ya kuma kyautata halittarta.
Duk wanda zai yi tunani, to zai riski
haqiqanin gaskiyar lamari.
Kuma ga Allah ne mulkin
sammai da qasa yake. Kuma
Allah Mai iko ne a kan komai.
Lalle a cikin halittar sammai
da qasa da sassavawar dare da
rana, tabbas akwai ayoyi ga
ma’abota hankula. [Ali Imran:
189-190]
Duniya gabaxayanta tana gudana ne bisa
wani tsari mai ban-mamaki wanda ba ya
kaucewa. Don haka duk wanda zai yi
tuntuntuni, to zai fahimci cewa, a cikin
hakan akwai wata qudira da take gudanar
da ita wadda ta qarfin qudirar mutum.
Ana ganin haqiqanin gaskiya ne tun kafin
ma a faxeta da baki.
Ba da daxewa ba za Mu nuna
musu ayoyinmu a cikin
nahiyoyi da kuma a kan
kawunansu har sai sun gane
cewa lalle shi (Alqur’ani)
gaskiya ne. Yanzu bai ishe ka
ba game da Ubangijinka cewa
Shi lalle Mai shaida ne a kan
komai? [Fussilat: 53]
Duk lokacin da ka yi tunani game da
halittar duniya, hakanan duk lokacin da
ka kalli kanka, za ka ji cewa lallai gaskiya
ba a nesa take ba a kusa take.
Akwai wata voyayyiyar murya da take yi
maka jagora zuwa ga samun yaqini, kai
dai kawai ka buxe mata zuciyarka.
Ba da daxewa ba za Mu nuna
musu ayoyinmu a cikin
nahiyoyi da kuma a kan
kawunansu har sai sun gane
cewa lalle shi (Alqur’ani)
gaskiya ne. Yanzu bai ishe ka
ba game da Ubangijinka cewa
Shi lalle Mai shaida ne a kan
komai? [Fussilat: 53]
A cikin kowane yanayi na sassan duniya,
hakanan a cikin kowane bugun zuciyarka
akwai wata alama da take ce maka, ba fa
kai kaxai ba ne.
Allah yana nuna maka abin da kake
buqata don ka san hanya.
Wanda Ya halicci sammai
bakwai hawa-hawa; ba za ka
ga wata tangarxa cikin halittar
(Allah) Mai rahama ba. Ka
maimaita dubanka, shin za ka
ga wata tsaga? [Mulk: 3]
Ya isheka ka yi duba zuwa halittar
sammai don ka ga irin tsarin da aka
xorasu a kai wanda babu wata tawaya da
ta haxu dashi.
Halitta ce da aka kyautata, tana yi maka
raxa da cewa, Hannun Allah Mai rahama,
babu tawaya a tattare da shi.
Wanda Ya halicci sammai
bakwai hawa-hawa; ba za ka
ga wata tangarxa cikin halittar
(Allah) Mai rahama ba. Ka
maimaita dubanka, shin za ka
ga wata tsaga? [Mulk: 3]
Yayin da za ka qara mayar da ganinka
zuwa sama bayan wanda ka yi a baya, ba
za ka tava ganin wata tawaya ko rashin
tsari ba a tattare da halittarta ba.
Don haka duniya gaba xayanta tana baka
labari cewa, wanda ya halicceta cikakke
ne cikin abin da ya halitta.
Waxanda kuwa suka nisanci
bautar xagutu, suka kuma
koma ga Allah, suna da
albishir (na Aljanna). To ka yi
wa bayina aibishir. Waxanda
suke sauraron magana sai su
bi mafi kyawunta, waxannan
su ne waxanda Allah Ya
shiriya, kuma waxannan su ne
ma’abota hankula. [Zumar:
17-18]
A yayin da mutum ya tsarkake zuciyarsa
daga dukkan abin da zai iya vatar dashi, ya koma zuwa ga Allah komawa ta
gaskiya, to Allah zai buxe masa qofa, ya
kuma lulluve shi da bushara, ya kuma ja
shi zuwa ga mafi tsaftar hanyar gaskiya.
Waxanda kuwa suka nisanci
bautar xagutu, suka kuma
koma ga Allah, suna da
albishir (na Aljanna). To ka yi
wa bayina aibishir. Waxanda
suke sauraron magana sai su
bi mafi kyawunta, waxannan
su ne waxanda Allah Ya
shiriya, kuma waxannan su ne
ma’abota hankula. [Zumar:
17-18]
Shiriya ba ta wanda yake yawan saurare
ba ce, a’a shiriya ta wanda yake iya
bambance alheri ne, ya kuma yi riqo da
mafi kyawunsa.
Irin waxannan su ne waxanda Allah ya ba
su hankali tsaftatacce da basirar da ba ta
kauce wa hanyar gaskiya.
Shin ba za su yi zuzzurfan
tunani game da ayoyin
Alqur’ani ba ne? Kuma da a
ce ya kasance daga wajen wani
yake ba Allah ba, tabbas da
sun sami savani mai yawa a
cikinsa. [Nisa’i: 82]
Aya xaya a cikin Alqur’ani ta isa buxe
qofar haske. Kuma duk wanda ya yi
tuntuntuni game da ita da gaske zai ga
tsarin da xan’adam ba zai iya kawo shi
ba.
Shin ba za su yi zuzzurfan
tunani game da ayoyin
Alqur’ani ba ne? Kuma da a
ce ya kasance daga wajen wani
yake ba Allah ba, tabbas da
sun sami savani mai yawa a
cikinsa. [Nisa’i: 82]
Gaskiya ba ta buqatar ado, ya isheka
kawai ka yi tunani game da ita domin
gane mavuvvugarta daga Allah take.
Ba za a tava samun littafin da babu savani
a cikinsa ba, sai dai idan daga Allah yake.
“(Su ne) waxanda suka yi
imani, zukatansu kuma suna
nutsuwa da ambaton Allah.
Ku saurara, da ambaton Allah
ne zukata suke nutsuwa.
[Ra’ad: 28]
Akwai lokutan da zuciya da ba za ta
nutsu ta daina raurawa ba a cikinsu, har
sai bawa ya ambaci Ubangijinsa, to a
lokacin ne nutsuwa za ta dawo, ya
zamana kamar dama tana dakon kira ne.
“(Su ne) waxanda suka yi
imani, zukatansu kuma suna
nutsuwa da ambaton Allah.
Ku saurara, da ambaton Allah
ne zukata suke nutsuwa.
[Ra’ad: 28]
Samun hutu ba a cikin canjin yanayi yake
ba, sai dai yana cikin alaqar zuciya da
Ubangijinta. Don haka yayin da za a
ambaci Allah, to dukkan abin da ya rikice
a cikin ran mutum zai nutsu ya dawo
hayyacinsa.
Ya kuma arzuta shi ta inda ba
ya tsammani. Duk wanda
kuma ya dogara ga Allah to
Shi Ya ishe shi. Lalle Allah
Mai zartar da al'amarinsa ne.
Haqiqa kuma Allah Ya sanya
iyaka ga kowane abu. [Xalaq:
3]
Arziqi yana zuwa ta inda mutum ba ya
tsammani. Don haka idan ka dogara ga
Allah da gaske, to Allah zai isar maka, ya
ba ka sama da abin da kake fatan ka
samu.
Ya kuma arzuta shi ta inda ba
ya tsammani. Duk wanda
kuma ya dogara ga Allah to
Shi Ya ishe shi. Lalle Allah
Mai zartar da al'amarinsa ne.
Haqiqa kuma Allah Ya sanya
iyaka ga kowane abu. [Xalaq:
3]
Duk wanda ya miqa lamarinsa ga Allah,
to zai ga qofofin alheri suna ta buxe masa
ba tare da wani sababi na zahiri ba.
Kowane abu yana wurin Allah da
ma’auni kyautatacce da iyakar da ba za ta sauya ba.