Islami Addini na amana da alhaki

Halifanci a bayan kasa nauyi ne, ba karramawa ba ce kadai. An halicci mutum don ya gina duniya, ba don ya batata ba, don ya tsayar da adalci ba don ya zubar da jini ba. Ka zamo halifa na gaskiya kamar yadda Allah yake so ka zama.
Ba matsayinka bane abin lura, a’a abin lura shi ne abin da kake aikatawa da matsayin. An halicceka don wani babban sako. Shin za ka zamo cikin masu gyara ko za ka zamo cikin masu varna.

Ilimin Halin Rai a cikin Alkur’ani Mai Tsarki

Ka yi tuntuntuni game da girman amana wadda sammai da kasa da duwatsu suka ki yarda su dauketa...amma a haka mutum ya karbeta, sai dai shi mai yawan zalintar kansa ne, mai yawan jahiltar karshen lamarinsa ne.
Amana nauyi ne mai girma da Allah ya bijirar dashi ga manyan halittu, amma suka ki yarda su karba, amma dan’adam yayi jara’a ya dauketa!

Gajerun bidiyoyi

verses