Mafi kyawun alqawari a rayuwarka shi ne, Allah Ta’ala ya ce, ku roqe Ni.
Babu sa wurin haxuwa tsakaninka da shi, hakanan babu xan tsakiya ko kuma kofar da aka rufe tsakaninka da shi.
Ubangijinku kuma Ya ce: “Ku roqe Ni zan amsa muku. Lalle waxanda suke yin girman kai game da bauta min, ba da daxewa ba za su shiga Jahannama a wulaqance.” Allah ne wanda Ya halitta muku dare don ku natsu a cikinsa, rana kuma don ku ga (yadda za ku yi harka). Lalle Allah Mai falala ne ga mutane, sai dai kuma yawancinsu ba sa godewa.
[Ghafir: 60-61]

Ba a samun galaba a kanmu saboda mu raunana ne, sai dai ana cin galaba a kanmu ne saboda muna dakatawa ga barin yin aaddu’a.
Yayin da za ka xaga hannayenka don yin addu’a, to ka sani fa ba kai kaxai ba ne.
“Kuma Ka rubuta mana kyakkyawan abu a cikin wannan duniyar, haka ma a lahira, lalle mu mun tuba zuwa gare Ka.” (Allah) Ya ce: “Ina saukar da azabata a kan wanda Na ga dama; rahamata kuwa ta yalwaci komai. Don haka da sannu zan rubuta ta ga waxanda suke kiyaye dokokin Allah, kuma suke bayar da zakka da kuma waxanda suke yin imani da ayoyinmu.
[A’araf: 156]
Rahamar Allah ba kamilallu cikakku take nema ba, a’a tana neman waxanda suke tuba ne. Saboda haka ne ma Allah Ta’ala yake cewa: “Rahamata kuwa ta yalwaci komai”.
“Kuma Ka rubuta mana kyakkyawan abu a cikin wannan duniyar, haka ma a lahira, lalle mu mun tuba zuwa gare Ka.” (Allah) Ya ce: “Ina saukar da azabata a kan wanda Na ga dama; rahamata kuwa ta yalwaci komai. Don haka da sannu zan rubuta ta ga waxanda suke kiyaye dokokin Allah, kuma suke bayar da zakka da kuma waxanda suke yin imani da ayoyinmu.
[A’araf: 156]
Da a ce mutane sun san yalwar rahamar Allah, to da sun yi kuka saboda samun kyakkyawan fata ba don tsoro ba.
Lalle Ubangijinku Shi ne Allah wanda Ya halicci sammai da qasa cikin kwana shida, sannan Ya daidaita a kan Al’arshi; Yana tsara al’amari (yadda Ya ga dama). Babu wani mai ceto sai da izininsa. Wannan Shi ne Allah Ubangijinku. To sai ku bauta masa. Ashe ba za ku wa’azantu ba?
[Yunus: 3]
Hutu mafi girma a rayuwa shi ne ka san cewa Allah ne ke tsara dukkan komai. Ba dukkan abin da yake faruwa ne wanda bai yi maka dadi ba, sashinsa zai yi maka jagora zuwa ga alheri.
Lalle Ubangijinku Shi ne Allah wanda Ya halicci sammai da qasa cikin kwana shida, sannan Ya daidaita a kan Al’arshi; Yana tsara al’amari (yadda Ya ga dama). Babu wani mai ceto sai da izininsa. Wannan Shi ne Allah Ubangijinku. To sai ku bauta masa. Ashe ba za ku wa’azantu ba?
[Yunus: 3]
Ka nutsu, abubuwan da kake ji ba sa yi maka daxi a yau, su ma suna cikin abin da Allah Ta’ala ya tsara.
Wane ne ya fi zalunci kamar wanda ya qaga wa Allah qarya ko kuma ya qaryata gaskiya lokacin da ta zo masa? Yanzu ashe babu mazaunar kafirai a cikin Jahannama? Waxanda kuma suka yi jihadi saboda Mu to tabbas za Mu shiryar da su hanyoyinmu, kuma lalle Allah Yana tare da masu kyautatawa.
[Ankabut: 68-69]
Abu mafi haxari shi ne ka yi wa Allah qarya ko ka qi karvar gaskiya bayan ka san gaskiyar ce.
Yin hakan ba zunubi ne da za a yi ya zo ya wuce ba, a’a yin hakan hanya ce mai duhu wanda makomarsa a bayyane take.
Wane ne ya fi zalunci kamar wanda ya qaga wa Allah qarya ko kuma ya qaryata gaskiya lokacin da ta zo masa? Yanzu ashe babu mazaunar kafirai a cikin Jahannama? Waxanda kuma suka yi jihadi saboda Mu to tabbas za Mu shiryar da su hanyoyinmu, kuma lalle Allah Yana tare da masu kyautatawa.
[Ankabut: 68-69]
Sai dai dukkan wani taqi na gaskiya da za a yi na kusantar Allah, to akwai shiriya mafi girma da za a samu.
Ka yaqi kanka, da sannu Allah zai buxe maka qofofin da ba ka yi tsammani ba.
Lalle Allah Ya sayi rayuka da dukiyoyin muminai daga wurinsu cewa suna da Aljanna: Za su yi yaqi saboda Allah, sai su kashe su ma kuma a kashe su. Alqawari ne na gaskiya da Ya xaukar wa kansa a cikin Attaura da Linjila da Alqur’ani. Wane ne ya fi Allah cika alqawarinsa? Saboda haka sai ku yi farin ciki da cinikin nan naku da kuka yi da Shi. Wannan kuwa shi ne rabo mai girma.
[Tauba: 111]
Ka yi tunani a ranka cewa, Allah ya sayi ranka da dukiyarka daga gareka, kuma kudin da aka biyaka da shi shi ne Aljanna.
Cinikin da babu asara a cikinsa har abada, amma fa idan ka gaskata da hakan.
Lalle Allah Ya sayi rayuka da dukiyoyin muminai daga wurinsu cewa suna da Aljanna: Za su yi yaqi saboda Allah, sai su kashe su ma kuma a kashe su. Alqawari ne na gaskiya da Ya xaukar wa kansa a cikin Attaura da Linjila da Alqur’ani. Wane ne ya fi Allah cika alqawarinsa? Saboda haka sai ku yi farin ciki da cinikin nan naku da kuka yi da Shi. Wannan kuwa shi ne rabo mai girma.
[Tauba: 111]
Ba sadaukarwa ba ce, sai dai kasuwanci ne tare da Allah.
Dukkan wata gajiya, hakanan dukkan wani abu da za a bayar, yana nan a taskace a wurin wanda ba ya sava alqawari.
Kuma ku yi gaggawa zuwa ga neman gafara ta musamman daga wajen Ubangijinku, da kuma Aljanna wadda faxinta yake daidai da sammai da qasa, an yi tanadinta domin masu taqawa. Su ne waxanda suke ciyarwa a cikin halin yalwa da halin qunci, kuma masu voye fushi kuma masu yin afuwa ga mutane. Allah kuwa Yana son masu kyautatawa.
[Ali Imran: 133-134]
Aljanna ba a nesa take ba, sai dai tana buqatar yalwatacciyar zuciya.
Wanda yake bayarwa yayin da yake cikin qunci, yake kuma voye fushi, yake kuma yin afuwa duk da yana da ikon xaukar fansa.
Kuma ku yi gaggawa zuwa ga neman gafara ta musamman daga wajen Ubangijinku, da kuma Aljanna wadda faxinta yake daidai da sammai da qasa, an yi tanadinta domin masu taqawa. Su ne waxanda suke ciyarwa a cikin halin yalwa da halin qunci, kuma masu voye fushi kuma masu yin afuwa ga mutane. Allah kuwa Yana son masu kyautatawa.
[Ali Imran: 133-134]
Mutum mafi qarfi ba shi ne wanda yake galaba a kan mutane ba, a’a mutum mafi qarfi shi ne wanda yake fin qarfin kansa yayin da ya yi fushi, yake zavar ya yi afuwa. To a sannan ne Allah zai soka.
Waxanda suka zauna a gida daga cikin muminai ba su fita yaqi ba, in dai ba masu larura ba, ba za su yi daidai da masu jihadi don xaukaka kalmar Allah da dukiyoyinsu da kawunansu ba. Allah Ya fifita darajar masu jihadi da dukiyoyinsu da kawunansu a kan waxanda suka zauna a gida. Kuma dukkansu Allah Ya yi masu alqawarin Aljanna. Kuma Allah Ya fifita masu jihadi a kan waxanda suka zauna a gida, da lada mai girma.
[Nisa’i: 95]
Mutane ba xaya suke ba, akwai wanda yake wadatuwa da abin da ya bayyana a gare shi. Akwai kuma wanda yake motsawa yake sadaukar da kansa. Bambancin kuma darajoji ne a wurin Allah.
Waxanda suka zauna a gida daga cikin muminai ba su fita yaqi ba, in dai ba masu larura ba, ba za su yi daidai da masu jihadi don xaukaka kalmar Allah da dukiyoyinsu da kawunansu ba. Allah Ya fifita darajar masu jihadi da dukiyoyinsu da kawunansu a kan waxanda suka zauna a gida. Kuma dukkansu Allah Ya yi masu alqawarin Aljanna. Kuma Allah Ya fifita masu jihadi a kan waxanda suka zauna a gida, da lada mai girma.
[Nisa’i: 95]
Ko da ba ba ka samu dama ba, to niyyarka ta gaskiya za ta iya xaukaka ka. Amma kuma idan ka samu damar kuma ka yi qoqarin yin aiki, to ladan da za ka samu zai zama mai girma sama da yadda kake tunani.
Muhammadu Manzon Allah ne. waxanda kuma suke tare da shi masu tsanani ne a kan kafirai, kuma masu tausayin junansu ne; za ka gan su suna ruku’i suna sujjada suna neman falala daga Allah da yardarsa; alamominsu na gurbin sujjada suna bayyana a fuskokinsu. Wannan shi ne misalinsu a cikin Attaura. Misalinsu kuwa a cikin Linjila kamar shuka ce da ta fitar da reshenta sai ya qarfafe ta, sannan ta yi kauri sai ta daidaita a kan tushiyarta ta riqa qayatar da manoma, don Ya cusa wa kafirai haushi. Allah Ya yi wa waxanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka nagari daga cikinsu alqawarin gafara da lada mai girma.
[Fat’h: 29]
Wannan ba kwatance ba ne ba kawai, sai dai hakan abin buga misali ne na mutum.
Qarfi ne da ya tunkari varna, rahama a tsakanin mutane da zuciyar da ta rataya fatanta ga Allah.
Muhammadu Manzon Allah ne. waxanda kuma suke tare da shi masu tsanani ne a kan kafirai, kuma masu tausayin junansu ne; za ka gan su suna ruku’i suna sujjada suna neman falala daga Allah da yardarsa; alamominsu na gurbin sujjada suna bayyana a fuskokinsu. Wannan shi ne misalinsu a cikin Attaura. Misalinsu kuwa a cikin Linjila kamar shuka ce da ta fitar da reshenta sai ya qarfafe ta, sannan ta yi kauri sai ta daidaita a kan tushiyarta ta riqa qayatar da manoma, don Ya cusa wa kafirai haushi. Allah Ya yi wa waxanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka nagari daga cikinsu alqawarin gafara da lada mai girma.
[Fat’h: 29]
Ka duba da kyau...
Addinin da yake samar da mutumin da ya haxa tsakanin qarfi da tausayi da ibada.
Ba tsattsauran ra’ayi ba ne, a’a daidaito ne da mutum ba zai iya samar da shi ba.
Mala’iku da Jibrilu suna ta saukowa da dukkanin al’amura a cikinsa da izinin Ubangijinsu. Aminci ne shi (daren dukkansa) har zuwa hudowar alfijir.
[Qadr: 4-5]
A dare guda mala’iku suna sauka zuwa saman duniya.
Aminci yana cika duniya har zuwa hudowar alfijir.
Abubuwa ne da ba a iya gani, amma kuma gaskiya ne.
Mala’iku da Jibrilu suna ta saukowa da dukkanin al’amura a cikinsa da izinin Ubangijinsu. Aminci ne shi (daren dukkansa) har zuwa hudowar alfijir.
[Qadr: 4-5]
Ba kowane abu ne na gaske ake iya ganinsa da ido ba. Akwai duniya cikakkiya da take gudana da izinin Allah, amma kuma kai ba ka sani ba.
Nutsuwar da kake nema za ta iya kasancewa tana kusa sama da yadda kake zato.
Kuma al’amarinmu bai zamanto ba face kalma xaya kamar qiftawar ido. Haqiqa kuma Mun hallakar da ire-irenku, to ko akwai mai wa’azantuwa? Kuma kowane abu da suka aikata yana cikin littattafai. Kowane qaramin abu da babba kuma suna nan a rubuce. Lalle masu taqawa suna cikin gidajen Aljanna da qoramu.
[Qamar: 50-54]
Al’amarin Allah ba ya buqatar xaukar dogon lokaci. Xan lokaci qanqani ya isa ya canja komai.
Kuma al’amarinmu bai zamanto ba face kalma xaya kamar qiftawar ido. Haqiqa kuma Mun hallakar da ire-irenku, to ko akwai mai wa’azantuwa? Kuma kowane abu da suka aikata yana cikin littattafai. Kowane qaramin abu da babba kuma suna nan a rubuce. Lalle masu taqawa suna cikin gidajen Aljanna da qoramu.
[Qamar: 50-54]
Komai a rubuce yake a littafi tun daga qarami har babba.
Ba rayuwa ba ce da ake yi ba kawai, a’a labari ne da aka rubuce a kyautace.
Me kake so a rubuta game da kai?
Yana shirya al’amari daga sama zuwa qasa sannan (al’amarin) ya hau zuwa gare Shi a cikin wani yini da gwargwadon (tsawonsa) yake shekara dubu ne daga abin da kuke qirgawa. Wannan (Shi ne) Masanin voye da sarari, Mabuwayi, Mai rahama.
[Sajda: 5-6]
Al’amarin Allah ba ya buqatar sai an xauki shekaru ana shirya shi, hakanan ba ya buqatar sai an samu dubban sabuba kafin ya auku.
Umarni ne guda xaya kawai, amma kuma da shi komai zai canja.
Rayuwa da arziqi da rashin lafiya da samun tsira da shiriya, dukkansu suna faruwa ne da kalma xaya tak.
Yana shirya al’amari daga sama zuwa qasa sannan (al’amarin) ya hau zuwa gare Shi a cikin wani yini da gwargwadon (tsawonsa) yake shekara dubu ne daga abin da kuke qirgawa. Wannan (Shi ne) Masanin voye da sarari, Mabuwayi, Mai rahama.
[Sajda: 5-6]
Kowane abu a rubuce yake a littafi, ba wai iya manyan ayyukanka ba. Har kalmomin da kake furtawa, har niyyoyin da kake qudurcewa, hakanan har abubuwan da riga ka aika ka manta da su.
Rayuwarka ba kwanaki ba ne da suke shuxewa ba kawai, a’a littafi ne da ake rubutawa game da kai.
To ya kake so taken labarinka ya kasance?