Allah ne wanda Ya sanya muku qasa ta zama wurin zama, sama kuma ta zama rufi, Ya kuma suranta ku, sai Ya kyautata surorinku, Ya kuma arzuta ku da daxaxan abubuwa. Wannan fa Shi ne Allah Ubangijinku. To Allah Ubangijin talikai albarkatunsa sun yawaita.”
[Ghafir: 64]
Kyawun da ke cikin halittarka, hakanan arziqin da ke kewaye da kai, wasu abubuwa ne da suke yi maka bayanin cewa, ba a bar ka haka kawai sakakai ba a wannan duniyar.
- Ka yi tunani
- #Arziqi
- #Samur_halitta